Shimfidar Aure na biyu 2

. SHIMFIDAR AURE
               ( FITOWA NA BIYU )

               Baby moon🌙

 "Sory my dear yau na gajiyar da kai..tana fada tana kallona hade da murmushi.
       Ba komai nima na mayar mata da murmushi idona kafe akan wani zobe da ke makale a dan ya tsanta.
 Lokaci guda sai muka hada ido, awannan karon ita kade take karfafa murmushi yayin da ni na nitse cikin lallausar mazaunin motar. Ta dan kada yatsar ta sannan ta tabe baki.
      Yana da daraja tace dani yayin da take murza dan zoben a hannunta. sannan sai naga ta kama ta cire shi, yana sheki cikin tafin hannunta. Ya naga kin cire nima na tambaya? Fuskata cike da mamaki.
     Nawane kuma zanyi kyauta ga wanda yake da matsayi aguna, ba dan ina iya biyanshi kulawa da yake min bane sai kawai na kwatan ta kaunata agare shi......bata gama fadar abin da take fada ba sai kawai naji jajayan yatsunta suna masu baiyana cikin tafin hannu na tare da mika min zoben sannan da hankali sai naji ta zame yatsunta tana gani na ido cikin ido ga mamakina, sai na kalli shekin kwalla cikin kyawun idanunta.
           Ya haka MARYAM naga kin mika min abu mai kima haka....Sai tayi fari da idanunta nawane na bawa wanda nake kauna..ka rike yananan ne kamar zuciya ta na kuma damka maka tamkar wata amanace agunka....Tana magana yayin da take raba sitbelt din motar da jikinta... Ka dawo ta nan ka mai da ni gida my dear ...zanyi magana sai ta min alama da dan yatsarta kar ka damu ni taka ce ko a lahirane da yardar Allah...
           Wannan kalmomi nata na karshe su suka jawo hankalina naji limanin unguwar mu yana cewa ALLHU AKHBAR da alama an shiga sallar asubahine..ni kuma ashe duk hakan na faruwa da nine cikin zurfin tunani da ya rikide ya zama mafarki.
         Cikin sauri na warci buta Dan hanzarta alwala...

 ****               ****                   ****                      ****

            Bayan mun idar da sallane na doshi gida Dan nayi kokarin kammala shirina na zuwa makaranta kasancewar ina da tex kuma da wasu lectures agabana.
      Ban kammala ba sai naji an sake kiran wayar MARYAM cikin sauri nasa hannu na dauka sannan na kara ta da kunne na, muryar da naji tamin sallama yayi matukar canza tunani ba dan komai ba kuwa sai jin muryar tayi kama da muryar wacce ta min kyautar zobe cikin mafarki na.
     Wa'alakumussalam nima na mayar mata... Dan Allah ina maganane da Wanda ya tsinci wannan wayar ta tambaya bayan mun gaisa
            Eh nine...nace da ita.
 Zanci gaba...

Comments

Popular posts from this blog

SHINFIDAR AURE