Shimfidar Aure na biyu 2
. SHIMFIDAR AURE ( FITOWA NA BIYU ) Baby moon🌙 "Sory my dear yau na gajiyar da kai..tana fada tana kallona hade da murmushi. Ba komai nima na mayar mata da murmushi idona kafe akan wani zobe da ke makale a dan ya tsanta. Lokaci guda sai muka hada ido, awannan karon ita kade take karfafa murmushi yayin da ni na nitse cikin lallausar mazaunin motar. Ta dan kada yatsar ta sannan ta tabe baki. Yana da daraja tace dani yayin da take murza dan zoben a hannunta. sannan sai naga ta kama ta cire shi, yana sheki cikin tafin hannunta. Ya naga kin cire nima na tambaya? Fuskata cike da mamaki. Nawane kuma zanyi kyauta ga wanda yake da matsayi aguna, ba dan ina iya biyanshi kulawa da yake min bane sai kawai na kwatan ta kaunata agare shi......bata gama fadar abin da take fada ba sai kawai naji jajayan yatsunta suna masu baiyana cikin tafin hannu na tare da mika min zoben sannan da hankali sai naji ta zame yatsunta tana gani na ido cikin ido ga
Comments
Post a Comment