SHINFIDAR AURE

. SHIMFIDAR AURE

      "Na dukufa cikin sauri dan na isa gida da wuri ganin magriba ya tunkaro, amma sai ga mamaki na, wasu samari ne da suke zaune akan benci a bakin titi sai naga sun shagala da kallon sashin da nake amma dana kara kula da yadda suke tsananta kallon nasu sai na waiwaya bayana dan nima naga mai yake faruwa..SUBHANALLAH tsarki ya kara tabbata ga mahalicci, nace cikin zuciya ta.

             "Ba wani abu bane face wasu matasan yammata biyu da ba kasafai nake kallon irin su ba a zahiri sai a tv a irin tashoshinnan na kasar larabawa, kwatancan su kuwa bazai yuwu anan ba. Suma daga dukkan alamu sauri suke dan suna kokarin hawa a dedeta sawu ne cikin hanzari.
         Tashin su ke da wuya sai idanuna yaci karo da wata waya a inda a dedeta sahun ya tashi, daga dukkan alamu na yammatannan ne gashi kuma har sun bace.
          Sauri nayi na dauka dan nasan yadda zan sada shi ga mai ita, amma kash, sai wayar ta kasance akashe take babu chaji.

        Na iso gida ina mai sallama da gaisuwa ga mahaifiyata, bayan na sanya mukulli a dakina ina kokarin kokarin budewa kasancewa
 na tuzuru, nan take na sanya wayar a caji na fito dan na isa masallaci na sami salla a jam'i.
      Sai dana jira har akayi sallar isha'i a dalilin ina daukan karatu bayan sallar magarib
       Na shugo dakina sannan naci abincin dare daga nan sai na dauko wannan wayar dana tsinta ganin mai ita zai iya bugowa, ga mamaki na, ina budewa sai wasu tex suka shigo. Da sauri na bude na fara karantawa.
 DAN ALLAH DUK WANDA YA TSINCI WAYAR NAN YAYI KOKARIN DAWO MIN DA ITA, IDAN KUWA BAZAI IYA BA, TO YAYI HAKURI YA BANI SIM DA MEMORIN.
           Wannan shine abin dana iya karantawa cikin sakon, abin ya bani mamaki ganin wayar ta doshi N50,000 amma damuwar mai ita sim da memori, wannan yasanyani gulma dan ganin menene a cikin memorin, Bayan nima na maidawa mai sakon da cewa KAR YA DAMU ZANYI KOKARI NA NEMI IN DA YAKE.
   

 "Kallona ya soma, tarone na mutane cikin wata farfajiya daga dukkan alamu murnar
 saukar Qur'ani ake taya wasu matasan dalibai
 lokacin da aga gabatar da daliba ta farko sai mamaki ya tunkaro zuciya ta. Ba wata bace face daya daga cikin yammatannan da suka sace mana kallon mu dazu goshin magariba.

      Gaskiya ta tara baiwa dayawa nace cikin raina lokacin dana ji sautunta tana rera kira'a
 cikin tajwidi, suratul AD-DUKHAN ta karanta

   Nan take wajan ya dau kabbara lokacin da ta karisa. a haka de suma sauran mahaddatan suka ta rera karatun Qur'ani.
    Ina gama kallon wannan bidyon sai na shiga
 kallon hotuna, anan ne fa Nagano ta da danginta abin de sai shuru sabo da sun wuce nata kwatance anan.

      " MARYAM ALI..shine sunan ta, zuciya na yaci gaba da ambaton sunan, agefe daya kuma, ga tunanina sai na tsinci kaina kamar almara ake mun cikin kallona.

     Fili Ne mai fadin gaske, wai gani ga Maryam ina koya mata mota.
   Ta taka koloci sai ta rage giya sannan tayi burki, idon ta cikin idona.
       "Sory my dear yau na gajiyar da kai, tana magana tana murmushi.
 Ba komai, nace da ita, nima ina mayar mata cikin murmushi. sannan idona akan wani zobe
 dake makale a hannun ta.....

 "NA BAR KU DA SAURAN LABARIN SAI KU BIJIRO DA CI GABAN SHI A CIKIN ZUKATAN KU...🥀🥀🥀


 .

Comments

Popular posts from this blog

Shimfidar Aure na biyu 2