Posts

KUCI GABA DA DUNKULE HANNAYEN KU...

Image
Wani dattijo yayi wuf da wata danyan Budurwa dan shima yana so ya shiga daga ciki, kar ya zama an yi babu shi a wannan lokacin da samari suka gaza wajan aure da mako irin ta zamani, wai da sunan gudun almobazaranci, A gefe gudu kuma dattawan sai caraf suke tayi da yammata da su raya sunnar aure da hana zinace zinace da ya yawaita ta hanyar yaudara irin na samarin zamani... To wannan de kalubale gare ku samari masu dunkule hannu dan rowar tsiya."

Wannan itace budurwa da ta kwarance da sangame mazaje

Image

Shimfidar Aure na biyu 2

Image
. SHIMFIDAR AURE                ( FITOWA NA BIYU )                Baby moon🌙  "Sory my dear yau na gajiyar da kai..tana fada tana kallona hade da murmushi.        Ba komai nima na mayar mata da murmushi idona kafe akan wani zobe da ke makale a dan ya tsanta.  Lokaci guda sai muka hada ido, awannan karon ita kade take karfafa murmushi yayin da ni na nitse cikin lallausar mazaunin motar. Ta dan kada yatsar ta sannan ta tabe baki.       Yana da daraja tace dani yayin da take murza dan zoben a hannunta. sannan sai naga ta kama ta cire shi, yana sheki cikin tafin hannunta. Ya naga kin cire nima na tambaya? Fuskata cike da mamaki.      Nawane kuma zanyi kyauta ga wanda yake da matsayi aguna, ba dan ina iya biyanshi kulawa da yake min bane sai kawai na kwatan ta kaunata agare shi......bata gama fadar abin da take fada ba sai kawai naji jajayan yatsunta suna masu baiyana cikin tafin hannu na tare da mika min zoben sannan da hankali sai naji ta zame yatsunta tana gani na ido cikin ido ga

SHINFIDAR AURE

Image
. SHIMFIDAR AURE       "Na dukufa cikin sauri dan na isa gida da wuri ganin magriba ya tunkaro, amma sai ga mamaki na, wasu samari ne da suke zaune akan benci a bakin titi sai naga sun shagala da kallon sashin da nake amma dana kara kula da yadda suke tsananta kallon nasu sai na waiwaya bayana dan nima naga mai yake faruwa..SUBHANALLAH tsarki ya kara tabbata ga mahalicci, nace cikin zuciya ta.              "Ba wani abu bane face wasu matasan yammata biyu da ba kasafai nake kallon irin su ba a zahiri sai a tv a irin tashoshinnan na kasar larabawa, kwatancan su kuwa bazai yuwu anan ba. Suma daga dukkan alamu sauri suke dan suna kokarin hawa a dedeta sawu ne cikin hanzari.          Tashin su ke da wuya sai idanuna yaci karo da wata waya a inda a dedeta sahun ya tashi, daga dukkan alamu na yammatannan ne gashi kuma har sun bace.           Sauri nayi na dauka dan nasan yadda zan sada shi ga mai ita, amma kash, sai wayar ta kasance akashe take babu chaji.         Na iso gida ina ma
Image