. SHIMFIDAR AURE "Na dukufa cikin sauri dan na isa gida da wuri ganin magriba ya tunkaro, amma sai ga mamaki na, wasu samari ne da suke zaune akan benci a bakin titi sai naga sun shagala da kallon sashin da nake amma dana kara kula da yadda suke tsananta kallon nasu sai na waiwaya bayana dan nima naga mai yake faruwa..SUBHANALLAH tsarki ya kara tabbata ga mahalicci, nace cikin zuciya ta. "Ba wani abu bane face wasu matasan yammata biyu da ba kasafai nake kallon irin su ba a zahiri sai a tv a irin tashoshinnan na kasar larabawa, kwatancan su kuwa bazai yuwu anan ba. Suma daga dukkan alamu sauri suke dan suna kokarin hawa a dedeta sawu ne cikin hanzari. Tashin su ke da wuya sai idanuna yaci karo da wata waya a inda a dedeta sahun ya tashi, daga dukkan alamu na yammatannan ne gashi kuma har sun bace. Sauri nayi na dauka dan nasan yadda zan sada shi ga mai ita, amma kash, sai wayar ta kasance akashe take babu chaji. Na iso gida ina ma
Comments
Post a Comment